Luke 17

1Sai Yesu ya ce wa almajiransa, ‘Babu shakka akwai sanadodin tuntube da za su sa mu yin zunubi amma kaiton wanda shine sanadin su! 2Zai gwammaci a rataya masa dutsen nika a wuyansa, a jefar da shi a cikin teku fiye da wanda zai zama sanadiyar tuntube ga wadannan kananan.

3Ku kula da kanku. Idan dan’uwanka ya yi laifi, ka tsauta masa, in kuwa ya tuba ka yafe masa. 4Idan ya yi maka laifi sau bakwai a rana daya sa’annan ya juyo wurinka sau bakwai ya ce, ‘Na tuba,’ ya wajabta ka yafe masa!”

5Sai Manzannin suka ce wa Ubangiji, ‘Ka kara mana bangaskiya.’ 6Ubangiji kuwa ya ce, “In kuna da bangaskiya kamar kwayar mastad, za ku ce wa wannan durumin, ‘Ka tuge, ka kuma dasu a cikin teku,’ zai yi biyayya da ku.

7Amma wanene a cikinku, idan yana da bawa mai yin masa noma ko kiwon tumaki, da zarar ya dawo daga jeji, zai ce masa, ‘Maza zo ka zauna ka ci abinci’? 8Ba zai ce masa, ‘Ka shirya mani wani abu domin in ci ka kuma yi damara, ka yi mini hidima har in gama ci da sha. Bayan haka sai ka ci ka sha’?

9Ba zai yi wa bawan nan godiya ba domin ya yi biyayya da abubuwan da aka umarce shi ya yi, ko zai yi haka? 10Haka kuma, idan kuka bi duk abin da aka umarce ku, sai ku ce, ‘Mu bayi ne marasa amfani. Mun dai yi abin da yake wajibi ne kurum.’”

11Wata rana yana tafiya zuwa Urushalima, sai ya bi iyakar kasar Samariya da Galili. 12Yayin da yana shiga wani kauye kenan, sai wadansu kutare maza guda goma suka tarye shi suna tsaye daga nesa da shi 13sai suka daga murya suka ce, “Yesu, Ubangiji, ka yi mana jinkai.”

14Da ya gan su, ya ce masu, “Ku je ku nuna kanku a wurin firistoci.” Ya zama sa’adda suke tafiya, sai suka tsarkaka. 15Daya daga cikinsu da ya ga an warkar da shi, ya koma, yana ta daukaka Allah da murya mai karfi. 16Ya fadi a gaban Yesu, yana masa godiya. Shi kuwa Basamariye ne.

17Yesu ya amsa ya ce, “Ba goma ne aka tsarkake ba? Ina sauran taran? 18Babu wani da ya dawo ya girmama Allah sai wannan bakon kadai?” 19Sai ya ce masa, “Tashi, kayi tafiyarka. Bangaskiyarka ta warkar da kai.”

20Da Farisawa suka tambaye shi lokacin da mulkin Allah zai bayyana, Yesu ya amsa masu ya ce, “Mulkin Allah ba lura ake yi da shi ba. 21Ba kuwa za a ce, ‘Gashi nan!’ Ko kuwa, ‘Ga shi can ba!’ domin mulkin Allah yana tsaknaninku.”

22Yesu ya ce wa almajiran, “Kwanaki na zuwa da za ku yi begen ganin rana daya cikin ranakun Dan Mutum, amma ba zaku gani ba. 23Za su ce maku, ‘Duba can! ‘Duba nan!’ Amma kada ku je kuna dubawa, ko kuwa ku bi su. 24Kamar yadda walkiya take haskakawa daga wannan bangaren sararin sama zuwa wancan bangaren, haka ma dan mutum zai zama a ranar bayyanuwarsa.

25Amma lalle sai ya sha wahaloli dabam dabam tukuna, mutanen zamanin nan kuma su ki shi. 26Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka kuma zai faru a lokacin bayyanar Dan Mutum. 27Ana ci, ana sha, ana aure, ana aurarwa, har zuwa ga ranar da Nuhu ya shiga jirgi - ruwan tufana kuma ya zo, ya hallaka su duka.

28Haka ma aka yi a zamanin Lutu, ana ci, ana sha, ana saye, ana sayarwa, ana shuke-shuke da gine-gine. 29Amma a ranar da Lutu, ya fita daga Saduma, aka zubo wuta da kibiritu daga sama, aka hallaka su duka.

30Haka kuma zai zama a ranar bayyanuwar Dan Mutum. 31A ranar nan fa, wanda yake kan soro kada ya sauka domin daukan kayansa daga cikin gida. Haka kuma wanda yake gona kada ya dawo.

32Ku tuna fa da matar Lutu. 33Duk mai son ransa, zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa, zai same shi.

34Ina gaya maku, a wannan dare za a sami mutum biyu a gado daya. Za a dauka daya, a kuma bar dayan. 35Za a sami mata biyu suna nika tare. Za a dauka daya a bar daya.” 36[”Za a ga mutum biyu a gona. Za a dauki daya a bar daya.”]

Sai suka tambaye shi, “Ina, Ubangiji?” Sai ya ce masu, “Duk in da gangar jiki yake, a nan ungulai sukan taru.”

37

Copyright information for HauULB